Kannywood
Laila Za Ta Siyawa Matar Nan Me Kwana Akan Titi Gida
MASHA ALLAH: Laila Za Ta Siyawa Matar Nan Me Kwana Akan Titi Gida
Daga Fauziyya D. Sulaiman
Alhamdulillah, Hajiya Laylah Ali Othman ta bayar da umarnin a samo gida da zaa siyawa baiwar Allah nan wacce ta ke rayuwa akan titi da yaranta, wallahi na rasa ma abun da zan ce saboda farin ciki, don Allah ya sani da baiwar Allah na kwana araina, tun daran jiya na ce a samo mana gidan da za mu kama mata haya su bar kantiti, to yanzu dai haj. Laila ta ce siyan gida za a yi ba haya ba saboda idan an kama haya waye zai biya mata a gaba?
Allah ya sakawa Laila da alkairi ya bara ladan aikinnan na taimakon bayin Allahda ta ke yi, amin ya Allah.