Kannywood
Auren wuri maganin zinar wuri: Auren daya jawo cece kuce a shafukan sada zumunta
Hotunan wasu sabbin amare ya karade shafukan sada zumunta.
Sai dai kamar yadda wasu basa gani suyi shiru, tuni ake ta magana akai duba da karamin jikin da angon yake dashi.
Sai dai wani makusancin angon ya bayyana angon ba yaro bane, domin kuwa Shekarun sa 26, karamin jikin ne dai da yake dashi, a cewar sa.
An daura auren na su ne a ranar juma’ar data gabata a jihar Katsina


Muna masu fatan Alkhairi da daurewar zaman Lafiya Amin.







