Kannywood

An yi jana’izar dattijuwar fina-finan Kannywood Binta Ola a birnin Katsina, wadda Allah ya yi wa rasuwa

An yi jana’izar dattijuwar fina-finan Kannywood Binta Ola a birnin Katsina, wadda Allah ya yi wa rasuwa a daren Laraba bayan gajeriyar jinya.

Bayanan da BBC ta samu sun ce dattijuwar ta kammala shirye-shiryen gudanar da bikin Maulidi a safiyar Laraba, amma sai ta kamu da rashin lafiya da tsakar dare kuma ta rasu.

Binta na cikin mutanen da suka gudanar da wasannin kwaikwayo na daɓe a rediyo tun kafin fina-finan zamani na Kannywood.

Sai dai danginta ba su da tabbas game da shekarun haihuwarta.

https://youtu.be/SSDiwrAlbz8?si=v9vWzwtpqrnfLDZB

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button