Uncategorized
Allah Yayiwa Jaruma Hannatu Umar Rasuwa A Yau
Tsohuwar Jarumar Finafinan Hausa, Hannatu Umar Ta Rasu
A yau Lahadi, 20 ga Agusta, 2023, Allah ya yi wa tsohuwar jaruma a Kannywood, Hannatu Umar Sani, rasuwa.
Hannatu ta rasu a gidan yayar ta da ke unguwar Katampe a garin Abuja.
Wata majiya a gidan nasu ta faɗa wa mujallar Fim cewa Hannatu ta tashi lafiya ƙalau ya da safe, ta fito za ta je falo ta karya kumallo sai ta yanke jiki ta faɗi. Ƙarshen tafiyar kenan.
Majiyar ta ce an yi jana’izar ta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a babban masallacin ƙasa da ke Abuja.
Allah ya jiƙan ta da rahama, amin.








